Yadda Zaka Samu 2GB Akan N500 Alayinka Airtel Da Kuma Kira Tsawon Mintuna 15 Akan N100

Assalamu alaikum masoya wannan shafi mai albarka Nagarta.Com.Ng kullum yauma munzo muku da wata garabasa wanda muke ganin zakuji dadinta, Wannan garabasa masu amfani da layin Airtel sune zasu moreta wanda da katin N500 zaka samu 2GB da kuma mintuna 15 na kiran duk layin dake fadin Nigeria.

Kamar yadda muka fada wannan tsarin yana aikine alayin Airtel kuma sunan wannan tsari Airtel Binge wanda kwanan kamafani Airtel yagabatar da wannan tsari wanda kuma yau zamu nuna muku yadda ake amfani da tsarin Airtel Binge.

Yadda Ake Amfani Da Tsarin Airtel Binge

Airtel.Binge Tsarine na AIRTEL da ke  bawa wanda suke amfani da layin AIRTEL 2GB akan N500, Bayan ka saka katin N500, sai ka danna wađannan lambobi *141*504#, akan wayarka natake zaka samu wannan garabasa,

Amma saidai kash wannan tsari wato Airtel Binge baya dadewa kamar sauran tsarukan Airtel iyakar kwana daya kacal wato 24 Idan bakayi amfani Dashi cikin kwana dayaba to Airtel zasu kwashe data sai kasayi, Hakan yana nufin kasan yadda zakayi kakarar da data cikin awa 24.

Haka kuma kana iya yin kira a 11k/s wato za a cajeka N6.6 kenan akan duk minti đaya da za kayi wanda hakan zai baka damar yin har mintuna 15 a duk N100, wanda zaka kira duk wanda kakeso da wannan Airtime.

Yadda Ake Shiga Tsarin Airtel Binge

Domin shiga wannan tsarin sai kayi amfani da wannan lambobi *315# akan wayarka nantake zaka shiga

Wannan shine karshen wannan post wato Yadda Zaka Samu 2GB Akan N500 Alayin Airtel Da Kuma Kira Na Tsawon Mintuna 15 Akan N100,

Sai kukasance da Nagarta.Com.Ng domin samun abubuwa masu alaka da wannan sannan zaku iya iyayin comments aka San wannan post kokuma kukira mu kaitsaye, Mungode.

Leave a Comment